Gwamnatin Tarayya ta fara gyaran babban titin Abuja zuwa Kano cikin gaggawa

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ministan Ayyuka,  Nweze David Umahi, ya ƙaddamar da aikin gyaran hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Da yake jawabi a wajen taron, Ministan ya bayyana cewa aikin titin ya kasu kashi uku: Abuja zuwa Kaduna (Sashe na ɗaya), Kaduna zuwA Zariya (Sashe na biyu) da Zariya zuwa Kano (Sashe na uku).

Sashen Zaria zuwa Kano, an kammala shi sosai da sauran kimanin kilomita 17 kuma kwanan nan an faɗaɗa shi da kimanin kilomita 5.3 zuwa filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, Kano tare da fitulu masu amfani da hasken rana.

Kamfanin BUA ne ke kula da wannan. Kamfanin Messrs Julius Berger (Nig.) ne ke kula da sashen Kaduna zuwa Zaria.

Duk da haka, saboda tafiyar hawainiyar aiki a Sashe na ɗaya, Injiniya. Umahi ya gargaɗi ainihin ɗan kwangilar, Messrs Julius Berger da ya daina wasa da aiki, inda ya buƙaci ya maida hankali wajen gabatar da aikin bisa ga kwangilolin da aka sake dubawa na Naira biliyan 740, yana mai jaddada cewa ba za a sake yin nazari a kan hakan ba.

Ministan ya kuma bayyana cewa, idan kamfanin Messrs Julius Berger ba su son ci gaba da aikin a kan yadda da aka amince, su ma za su iya fitowa fili su faɗa, domin ma’aikatar a shirye take ta yi shi a kan kari, tare da ci gaba da gudanar da aiki mai inganci na babbar hanyar Legas – Calabar Coastal Highway ko Apapa – Oworonshoki Eɗpressway, wadda ake sa ran za ta yi tsawon shekaru 50 zuwa 100.

Injiniya Umahi ya kuma ci gaba da cewa, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin a ɗauki matakai guda biyu cikin gaggawa a kan hanyar domin sauƙaƙa wa masu amfani da hanyar, ayyukan da za a yi na rage raɗaɗi,” inji shi cikin raha.

By ukarofi