Na taɓa kurmancewa da kashi 25 ba tare da sani na ba – Obasanjo

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Tsohon shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo ya ce ya taɓa samun matsalar ji da kashi 25 cikin 100 ba tare da saninsa ba.

Obasanjo ya bayyana haka ne a Bauchi a ranar Lahadi a lokacin da ya kai wa Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Suleiman-Adamu ziyara.

A cewarsa, mutane da dama a duniya suna samun matsalar ji ba tare da sanin su ba har sai sun je a duba lafiyarsu kafin a bayyana musu.

Ya ba da labarin cewa, akwai lokacin da ya je ƙasar waje kuma ba ya jin magana sosai a lokacin da wani ke magana da shi, inda ya dage cewa babu wani abu da ke damun kunnuwansa, kuma mutumin ya nemi ya je a duba kunnuwansa.

Obasanjo ya ce sakamakon binciken da aka yi a asibiti ya nuna cewa kashi 25 cikin 100 kurma ne shi.

“Bayan sakamako na ya fito, sai na nemi mutumin da ya duba babban jami’in tsaro na a lokacin amma abin mamaki, ya fi ni kurmancewa,” inji shi.

Wannan gogewa, inji shi, ita ce ta kafa gidauniyar Olusegun Obasanjo, inda ya ƙara da cewa dubban ‘yan Njjeriya ne suka ci gajiyar jinyar kunne da kuma samar da na’urorin ji tare da haɗin gwiwar gidauniyar Starkey Hearing.

Tsohon shugaban ƙasar ya ce zai ƙaddamar da rabon kayayyakin da suka shafi kunne ga marasa galihu kusan 10,000 a yankin Arewa maso Gabas, wanda zai fara daga jihar Bauchi inda mutane 2,000 za su amfana.

Ya ce aikun mai taken: ‘Sound Interɓention Mission’ don ‘yan Nijeriya su riƙa ji sosai, za a aiwatar da shi a ƙarƙashin gidauniyar Obasanjo.

Obasanjo ya ci gaba da cewa dole ne kowa ya tashi tsaye wajen tunkarar ƙalubalen tsaro a ƙasar nan.

Yayin da yake mayar da martani, Sulriman-Adamu ya ce kasancewar Obasanjo a jihar wata alama ce ta jajircewarsa na ci gaban dukkanin yankunan ƙasar nan.

By ukarofi