Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Ɗan takarar Kansila a mazaɓar Fagge C dake ƙaramar hukumar Fagge, Hon. Sanusi Sharif Kantoma ya yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa tallafin kuɗi da ya bai wa ‘yan kasuwar Kantin Kwari sakamakon gobara da suka yi.
Ya ce ziyarar tausayawa da alhini da jaje da tallafin da gwamnan ya yi ga ‘yan kasuwar ya nuna irin tausayi da kulawa da yake ga al’ummar sa duk lokacinsa wani abu ya samesu.
Ɗan takarar Kansilan na mazaɓar Fagge C a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP ya yabawa al’ummar ƙaramar hukumar bisa goyon baya ga suka baiwa tsarin tafiyar Kwankwasiyya suka zaɓi Gwamna Abba Kabir Yusuf a jam’iyyar NNPP da sauran wakilan su na majalisun jiha dana tarayya.
Hon Sanusi Sharif Kantoma ya yi kira ga al’ummar Fagge da ma jihar Kano baki ɗaya akan su duba irin tagomashi da ayyuka da Gwamnatin jihar Kano take su fito su zaɓi yan takarar jam’iyyar NNPP na kowane mataki a zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli da ke tafe.
Ya gode wa al’ummar mazaɓar Fagge C da na ƙaramar hukumar Fagge baki ɗaya bisa goyon baya da suke bai wa tsarin tafiyar Kwabo ya yi fatan za su ƙara ba su goyon baya don cimma nasara a zaɓe mai zuwa.
Hon. Sanusi Sharu Kantoma ya yaba da irin goyon baya da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar NNPP a ƙaramar hukumar Fagge ke ba su tun daga kan shugaban jam’iyyar NNPP na Fagge, Alhaji Sulaiman Chamba da dattawan jam’iyyar da ‘yan majalisun su na tarayya Barista Muhammad Bello Shehu da na jiha Tukur Muhammad bisa haɗin kai da goyon baya da suke bai wa ɗan takararsu na shugaban ƙaramar hukumar Fagge da dukkan ‘yan takarar kansiloli na mazaɓun yankin.
