Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Mai martaba Sarkin Kano, Malam Muhammad Sanusi na biyu ya naɗa, Alhaji Auwalu Mudi Yakasai Sakataren ƙungiyar ƙwadago na jihar Kano a matsayin ɗanmalikin Kano.
Da yake zantawa da ‘yan jarida bayan naɗin da aka yi masa a ranar Juma’a da ta gabata a fadar Kano, Alhaji Auwal Mudi Yakasai ya bayyana godiyarsa ga Allah da kuma godiya ga Sarki Muhammad Sanusi bisa wannan naɗin da ya yi masa.
Ya ƙara da cewa a tarihin gidansu sun shafe sama da shekaru 130 rabon su da sarautar sai yanzu Allah ya waiwaye su, mai martaba Sarkin Kano ya waiwaye su ya dawo musu da wannan sarautar.
Ya yi nuni da ce wannan abin a yaba ne, a gode wa Sarkin Kano a yi masa addu’a, ba abinda za su ce sai “Allah ya taimaki Sarki, ya kare shi ya kyautata bayansa, kamar yadda ya waiwayi zuri’arsu, Allah ya waiwayi nasa ya ƙarawa mahaifiyarsa lafiya ya jiƙan mahaifinsa,” inji ɗanmalikin Kano.
Alhaji Auwal Mudi Yakasai ya yi nuni da cewa a cikin mutane, kowa yana da irin ƙaddarar sa, Allah ya ƙaddara shine zai ɗauko kitsen a wuta na samun wannan sarauta wanda Allah da ya ƙaddara hakan, shine kuma yasan me yake nufi akai ba su da abinda za su yi sai dai su cigaba da gode masa.
Alhaji Auwal Mudi Yakasai ya yi kira ga al’umma musamman matasa akan su ji tsoron Allah susa gaskiya a duk abinda suke sanan su girmama iyaye da shugabanci da shugabanni idan aka riƙe wannan za a zauna lafiya a sami cigaba da albarka a rayuwa.
Auwal Mudi Yakasai ya ce abinda za su sa a gaba a wannan sarauta shine alkhairi domin shi suka gada in Allah ya yarda shi za su cigaba da yi.
Sabon ɗan malikin na Kano, Alhaji Auwalu Mudi Yakasai ya ce aikin ɗanmaliki a fadar Sarkin Kano aikin Sarki ne, kuma shi Sarki ba a yi masa shisshigi a ayyukansa.
