
Daga BELLO A. BABAJI
Wata helikwafta a Fatakwal da ke Jihar Ribas ta yi hatsari wanda ya rutsa da ɗaya daga cikin jami’an kamfanin Man fetur na Ƙasa, NNPCL.
Kakakin kamfanin, Olufemi Soneye ya tabbatar da cewa, helikwaftar wadda kamfanin East Wind Aviation ke gudanar da ita ta kasance ta na aiki ne da NNPCL a lokacin da lamarin ya faru.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:22 na safe a wani yanki na taruka
da ke Fatakwal lokacin da jirgin ya tashi daga sansanin sojoji don zuwa tashar mai ta FPSO – NUIMS ANTAN.
Aƙalla mutane takwas ne lamarin wanda ya faru a yankin Bonny Finima na Tekun Atilantika, ya shafa inda tuni Ma’aikatar Sufurin Jiragen sama ta aika da tawagar gaggawa don ceto su, kamar yadda wata sanarwa daga kakakin ma’aikatar, Odutayo Olusheyi, ta nuna.
