Wasu takardun kuɗi za su daina aiki kafin ƙarshen shekara – Majalisar Wakilai

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Majalisar Wakilai ta yi kira ga Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya fara janye tsoffin takardun kuɗi na N200, N500, da N1,000 kafin wa’adin ranar 31 ga Disamba, 2024.

A zaman majalisar na ranar Alhamis, ƴan majalisar sun nemi CBN ya ƙara adadin da ya ke fitarwa na sabbin kuɗaɗe don tabbatar da sauyin kuɗi ya gudana ba tare da matsala ba.

Wannan ƙudiri ya biyo bayan ƙudirin gaggawa da Ɗan Majalisa, Afam Ogene ya gabatar, inda ya nuna damuwa kan rashin isasshen wayar da kan jama’a game da wa’adin da ke tafe.

Ogene ya lura cewa saura ƙasa da watanni biyu, CBN bai fara gudanar da wata babbar sanarwa ga jama’a ba, wani muhimmin mataki don kaucewa maimaita rikicin shekarar 2023 lokacin da sauyin kuɗi ya haifar da wahalhalu acikin al’umma.

Ya ƙara da cewa, idan CBN bai ɗauki matakin da ya dace ba na sanar da mutane halin da ake ciki, ƴan Nijeriya za su fuskanci matsaloli masu tsanani yayin da tsoffin kuɗaɗen za su daina aiki daga ranar 1 ga Janairu, 2025.

Ya kuma tunatar da rigingimu da fushin jama’a lokacin sauyin kuɗi na 2023, yana mai jaddada muhimmanci ɗaukar matakan da suka dace.

By Babaji