Daga USMAN KAROFI
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa za ta bi umarnin kotu da ta hana ta shiga cikin zaɓen ƙananan hukumomi da za a yi a ranar Asabar, 26 ga Oktoba, 2024.
Cikin wani saƙon bidiyo da mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna, ya fitar a ranar Juma’a, rundunar ta ce duk da haka, za ta tabbatar da tsaron rayuka a faɗin jihar.
“Muna bin umarnin kotu da ta hana mu shiga cikin zaɓen ƙananan hukumomi a jihar Kano. Duk da haka, za mu ci gaba da aiwatar da nauyinmu na kare rayuka da dukiyoyi,” in ji Haruna.
Bugu da ƙari, Kotu ta ba Hukumar Zaɓe ta Jihar Kano (KANSIEC) damar ci gaba da gudanar da zaɓen, inda tai watsi da ƙoƙarin wasu jam’iyyun siyasa na daƙile gudanar da zaɓukan.
Alƙalin kotun, Mai shari’a Sanusi Ma’aji, ya bayyana cewa dokar ƙasa ta bai wa KANSIEC damar gudanarwa, sa ido, da jagorantar zaɓen ƙananan hukumomi a dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar.
KANSIEC ta kuma tabbatar da shirye-shiryenta na gudanar da zaɓen kamar yadda aka tsara, tare da tabbatar da isasshen tsaro ga duk masu kaɗa kuri’a da mazauna jihar.
