Daga UMAR GARBA a Katsina
Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina ta cafke wani yaro ɗan shekara 16 mai suna Nuhu Haruna daga ƙaramar Hukumar Dutsinma bisa zargin kashe kishiyar mahaifiyarsa.
Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina ASP Abubakar Sadiƙ ne ya gabatar da yaron a gaban manema labarai tare da wasu da ake zargi da hannu wajen yin garkuwa da mutane da kuma kisan kai a jihar.
Kakakin rundunar, wanda ya gabatar da waɗanda ake zargin a hedikwatar rundunar ya bayyana cewa, an kama Haruna ne biyo bayan wata hatsaniya da suka yi da abokiyar zaman mahaifiyarsa Rabi Haruna mai shekaru 40, wanda hatsaniyar ta yi sanadin mutuwarta.
“A ranar 21 ga Oktoba, 2024, da misalin ƙarfe 1:00 na rana, rundunar ‘yan sanda ta kama wani Nuhu Haruna, mai shekaru 16, a ƙauyen Fenza, ƙaramar Hukumar Dutsinma, bisa laifin kisan kai,” inji ASP Sadiƙ.
“Wanda ake zargin ya daki mahaifiyarsa da sanda a cikinta a lokacin da aka samu rashin fahimtar juna a tsakaninsu, wanda hakan ya yi sanadiyar rasa ranta,’ inji Kakakin.
A wani labarin kuma, rundunar ‘yan sandan ta kuma cafke wani Abubakar Nasiru wanda aka fi sani da Haro daga ƙaramar Hukumar Daura bisa zarginsa da haɗa baki da kuma yin garkuwa da mutane.
ASP Sadiƙ ya bayyana cewa Nasiru wanda a baya aka taɓa ɗaure shi saboda laifin fyaɗe, yanzu kuma ana zarginsa da hannu wajen yin garkuwa da mutane.
Nasiru ya haɗa baki da wasu ɓatagari a shekarar 2023, inda suka kai hari ƙauyen Unguwar Mazadu dake ƙaramar Hukumar ƙafur, tare da yin garkuwa da mutane uku.
“An biya kuɗin fansa Naira miliyan 13 domin a sake su, inda Nasiru ya amsa cewa ya karɓi Naira miliyan 2 a matsayin kason sa,” in ji Kakakin rundunar.
Yanzu haka dai rundunar ta duƙufa wajen gano abokan laifin na sa kamar yadda ASP Abubakar Sadiƙ ya bayyana.
