Dan wasan gaba na Brazil da Real Madrid ɓinicius Jr ya ce zai ci gaba da yaƙi da wariyar launin fata duk da cewa fafutukarsa ce ta hana shi lashe kyautar Ballon d’Or ta bana, kamar yadda majiyoyi na kusa da ɗan wasan suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Vinicius wanda ya zo na biyu a lambar yabon mafi daraja na ƙwallon ƙafa wanda ɗan wasan tsakiya na Sifaniya da Manchester City Rodriguez ya lashe, ya ce zai ninka abin da ya ke har sau 10.
Kungiyarsa ta Real Madrid ta ƙauracewa halartar bikin bada ƙyautar ta Ballon d’Or a birnin Paris, bayan samun tabbacin cewa ɗan wasan na Brazil bazai lashe kyautar ba.
