Daga JAMEEL GULMA a Kebbi
A cikin shirinta na yaƙi da cututtuka da ke yaɗuwa tsakanin jama’a, uwargidan gwamnan jihar Kebbi Hajiya Zainab Nasir (Nasare) ta ƙaddamar da cibiyoyin gwaje-gwajen cututtukan hawan jini da ciwon siga ga marasa lafiya maza da mata marasa galihu a jihar Kebbi.
An ƙaddamar da shirin a garin mai taken “Ka San Lambarka Kuma Ka Kiyaye” a Gwadangaji da ke ƙaramar hukumar mulki ta Birnin Kebbi inda Hajiya Zainab ta bayyana cewa ana hasashen yi wa mutane milliyan goma faɗin ƙasar nan.
Da ta ke jawabi a madadin Uwargidan gwamnan Kebbi Hajiya Zainab, shugabar ma’aikatan jihar ta riƙon ƙwarya Hajiya A’isha Usman ta ce wannan shirin na ƙididdigewa shi ne zai bai wa wannan shirin damar sanin adadi da kuma yanayin matakin cutar don sanin irin maganin da ya kamata kowane mutum ya yi amfani da shi.
Ta nemi haɗin kan masu ruwa da tsaki tun kama daga hukumomin lafiya ya zuwa ƙungiyoyi masu zaman kansu a cikin wannan lamarin da su kara kaimi wajen shelanta illar wadannan cututtuka a kafafen yaɗa labarai da sauran hanyoyi.
Ta ƙara da cewa an buɗe cibiyoyin gwaje-gwajen waɗannan cututtuka a ƙananan hukumomi ashirin da ɗaya da ke faɗin jihar saboda a sauƙaƙa doguwar tafiya zuwa waɗansu asibitoci.
Da ya ke jawabi tun da farko a madadin Malam Sama’ila kwamishinan lafiya na jihar, babban Sakatare a ma’aikatar lafiya Dokta Nuhu Koko ya bayar da tabbacin gwamantin jihar Kebbi ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ɗabbaƙa wannan shirin, kuma za ta ɗauki duk matakin da ya dace don ganin an samu nasarar aiwatar da wannan aikin.
Uban ƙasar Diggi shi ne ya wakilci Sarkin Gwandu Manjo Muhammad Iliyasu Bashar (Murabus) ya jaddada goyon bayan wannan shirin a matakin masarauta kuma za su bayar da gudummawar da duk ta dace.
