Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Sabon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na shiyyar Kano ta Tsakiya, Alhaji Kabiru Bello Ɗandago ya ce zai gabatar da ayyukan da za su zama na samun cigaba ga jam’iyyar a jihar Kano.
Ya bayyana hakan ne a yayin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a shiryar Kano ta Tsakiya ya ce zaɓen fitar da shugabannin jam’iyyar da aka gudanar sun san ya yi wa wasu daɗi wasu kuma akasin haka, amma su a matsayinsu na sabbin shugabanni aikinsu na farko shine su yi rarrashi da bayar da haƙuri da saka cigaban jam’iyyar a gaba.
Alhaji Kabiru Bello Ɗandago ya ce a matsayinsa na shugaba a shiryar Kano ta Tsakiya a yayin da aka gudanar da zaɓe aka gama lafiya, shine babban nasara a garesu.
Ya yi jan hankali ga ‘yan jam’iyyar ta PDP su sani jam’iyyar ba ta shugabanni ba ce kaɗai ta duk ‘ya’yan jam’iyyar ne da kuma duk wanda ya amince da ita, hatta mai zaɓe in ya yarda da ita shi ma ya zama mai ruwa da tsaki a ciki.
ɗandago ya ce a 2015 da suka ce kar a kori jam’iyyar PDP sun san abinda ta tsara, amma mutanen Nijeriya suka ƙeƙashe ƙasa suka ƙi saboda yaudara da aka yi musu, ya ce yanzu kowa ya duba aljihunsa da tukunyarsa, mace a ɗakin mijinta ta faɗi irin ƙunci na zamantakewa da ta gani daga 2015 lokacin da PDP ta bar gwamnati zuwa yanzu a lokacin PDP ana sayar da buhun shinkafa N8,000 amma yanzu fa?
Alhaji Kabiru Bello Ɗandago ya yi kira ga al’ummar Kano da ƙasar nan su yi karatun tanatsu su sake jarraba jam’iyyar PDP za su ɗauke su daga inda APC ta kai ta ajiye su yanzu su mayar da su tashar da suka bar su, inda APC ta ɗauko su su kawo gyara da zai inganta cigaban rayuwar al’umma.
