Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon Darakta-Janar na Kwamitin Yain Neman Zaɓen Obi/Datti, Mista Doyin Okupe ya ce an ƙulla alƙawari cewa yankin Arewa zai mulki Nijeriya tsawon shekara takwas sannan yankin Kudu ya karɓa na tsawon shekara takwas.
Doyin Okupe ya bayyana cewa tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari daga yankin Arewa ya yi shekara takwas a bisa mulki, don haka Tinubu da ke kan mulki zai yi shekara takwas idan yana so.
Okupe wanda tsohon kakakin tsohon Shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ne, ya ce Tinubu na iya cin zaɓen Shugaban ƙasa a 2027 idan ya iya shawo kan matsalolin da ke damun Nijeriya a yanzu.
A yayin da ake hira da shi a shirin siyasan gidan talabijin na Channels, Okue ya ce, “Tinubu na yin abin da ayaba soja kuma nan gaba zai yi abin da ya fi hakan. Abin da yake buƙata shi ne a ƙara fahimtarsa ba yi masa zagon ƙasa ba.
“Idan ba a shiga wannan mawuyacin halin ba, watakila da ƙasar nan ta durƙushe, kuma na yi imanin idan aka ba shi ƙarin lokaci zai gyara ƙasar nan.
“‘Yan Nijeriya ne za su yi alƙalanci, kuma na tabbata san sun abin da ya kamata, kuma ba su takura wa shugabanni ba. Idan Tinubu ya magance matsalar man fetur da tsadar abinci kafin lokacin, mutane za su ce idan ba shi ba sai rijiya.
“Bola Tinubu ba sakarai ba ne, ya san idan bai yi hakan da kyau ba daga yanzu zuaw 2027 ba zai ƙara samun wata dama ba. A kasar nan an yi alƙawari cewa yankin Arewa zai yi shugabanci na shekara takwas sannan yankin Kudu ya yi takwas.
“Buhari bai taɓuka abin ƙwarai ba amma duk da haka ba mu haukace masa ba. Amma Tinubu na yin abin da ya dace, don haka zai yi shekara takwas idan Allah Ya ba shi tsawon kwanan kuma ya so.”
