Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wasu ’yan kasuwar man fetur uku, AYM Shafa, A. AA Rano, da Matrix sun buƙaci babbar kotun tarayya da ke Abuja da ta yi watsi da ƙarar da matatar man dangote ta shigar.
A cikin takardar shaidar haɗin gwiwa mai alamar: FHC/ABJ/CS/1324/2024, da kwanan wata Nuwamba 5, manyan ’yan kasuwa uku a Nijeriya sun buƙaci kotu da dakatar da Dangote daga mamaye ɓangaren mai a ƙasar.
Kamfanonin sun ɗauki matakin ne bayan Dangote ya yi ƙorafi a kwace lasisinsu na shigo da mai daga ƙetare.
Hakan ya biyo bayan zargin da Dangote ke yi musu kan shigo da mai marar inganci daga ƙasashen waje.
Lamarin ya sanya fargaba daga ɓangaren ’yan kasuwar da suke ganin Dangote na ƙoƙarin zama mai juya alakar komai a ɓangaren fetur.
‘Yan kasuwar suka ce, barin matatar Dangote mamaye ɓangaren zai kawo cikas ga cigaban Nijeriya.
Sun buƙaci Babbar Kotun Tarayya ta daƙile Dangote saboda zai zama shi kadai ke da iko a ɓangaren.
Har ila yau, suka ce bai kamata Dangote ya mayar da ɓangaren kaman na shi shi kaɗai ba, duba da yawan ’yan kasuwa da ake damawa da su.
