Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
’Yan fashin daji sun kona wasu gonakin masarar shida kafin a girbe su a ƙauyukan Kwaga da Unguwar Zako da ke ƙaramar Hukumar Birnin Gwari a Jihar Kaduna.
Danyen aikin ’yan ta’addan ya girgiza al’ummar ƙauyukan, musamman masu gonakin da abin ya shafa, inda suka rika nuna alhini.
Wakilinmu ya ga bidiyon irin ɓarnar da wutar da ’yan fashin dajin suka cinna ta yi a gonakin.
Daya daga cikin masu gonakin, Malam Kabiru Halilu Kwaga, ya shaida wa Manhaja cewa a bara ya noma buhu 160 na masara a gonar, kuma a bana yana kyautata zaton samun fiye da haka, amma maharan suka ƙona gonar.
Malam Surajo Kwaga kuma ya ce buhu 40 ya samu a gonar bara, amma bana an ƙone ta ɗungurungum.
Shi kuma Malam Dan Gido, da ya samu buhu 50 a bara, ya ce ya yi fatan samun kimanin buhu 65 a gonar a bana, amma kuma wannan abin ya faru.
Malam Jibril Kwaga da ya rasa amfanin gonarsa a wannan mummunan hari ya yi fatan Allah Ya mayar musu da mafi alheri.
Da yake tabbatar da lamarin, Shugaban ƙungiyar Masu Kishin Yankunan Birnin Gwari da ke Makwabtaka da Jihar Neja, Ishaƙ Usman Kasai, ya yi zargin cewa ’yan fashin dajin da suka kona gonakin, yaran dan ta’adda Yellow Jamburos ne, da suke addabar yankin.
Wakilinmu ya yi ƙoƙarin samun ƙarin bayani daga kakakin rundunar ’yan sanda na Jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, amma ya kasa samun jami’in a waya, har zuwa lokacin da muka kammala wannan labari.
