Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Aƙalla matasa 13 ne ake fargabar sun mutu bayan ruftawar ƙasa a wurin haƙar ma’adinai a ƙaramar Hukumar Bassa da ke Jihar Filato.
Manhaja ta lura cewa yawancin masu haƙar ma’adinan da suka rasu matasa ne masu shekaru 18 zuwa 30.
Shugaban ƙaramar hukumar, Dokta Joshua Riti, ya ce mutum bakwai daga cikin mamatan ’yan asalin ƙaramar hukumar ne.
Ya bayana cewa wurin haƙar ma’adinan da abin ya faru, ya yana kan iyakan ƙananan hukumomin Bassa, Jos ta Kudu da kuma Jos ta Arewa.
“Wannan abin takaici ne, matasa suna neman abin dogaro da kansu irin wannn ya rutsa da su.
“Sun fita suna aikin ƙarfi domin rufa wa kansu asiri a wannan lokaci da ake fama da matsin tattalin arziki, amma suka gamu da ajalinsu,” in ji Dokta Riti.
Daga nan ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalai da abokan arzikin da abin ya ritsa da su.
