Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban Kamfanin Man Fetur na ƙasa, NNPCL, Mele Kyari, ya jaddada aniyar kamfanin na magance matsalar makamashi da ‘yan Nijeriya ke fama da shi ta hanyar mai da hankali kan bunƙasa fannin makashin da samar da shi yadda ya kamata cikin farashi mai sauƙi.
A cewar wata sanarwar da jami’in yaɗa labarai na kamfanin ya fitar a ranar Litinin, Olufemi Soneye, ya ce, shugaban kamfanin ya ba da wannan tabbaci ne a yayin buɗe taron shekara-shekara na ƙara wa juna sani karo na 42 na ƙungiyar Masana Harkar Man Fetur (NAPE) da ake yi a jihar Legas.
Mista Kyari ya yi cikakken bayani kan burin Nijeriya ya inganta harkar makashi musamman batun ƙara yawan gas ɗin da ake samarwa a cikin gida.
A cikin jawabin nasa, Mele Kyari, ya bayyana shirin NNPC na ƙaddamar da manyan gidajen Iskar gas samfurin CNG 12 haɗi da na saufurin iskar gas ɗin LNG nan da ‘yan wasu watanni masu zuwa.
Ya ce wannan wani yunƙuri ne na inganta yawan gas ɗin da ake amfani da shi a ƙasar nan wanda a yanzu ana iya amfani ne da kubik biliyan 1.6.
Mista Kyari ya bayyana yunƙurin samar da tashoshin iskar gas ɗin a matsayin wani “nauyi” da ya rataya a wuyansu na ganin an ciyar da ɓangaren iskar gas gaba a Nijeriya.
“Wannan matsalar da aka samu kai a ciki, babban nauyi ne a kanmu mu ga mun inganta harkar makashi saboda gobenmu,” in ji Mele Kyari. Daga nan ya jaddada ƙoƙarin da suke yi na ganin an inganta tsarin samar da iskar gas da samar da sabbin hanyoyin tace shi da faɗaɗa kasuwancinsa.
Mr Kyari ya ce NNPC na ƙoƙarin faɗaɗa aikin shimfiɗa faife-faife na iskar gas kamar na Ajaokuta-Kaduna-Kano (AKK) da na Obiafu-Obrikom-Oben (OB3) domin rage batun shigo da iskar gas daga ƙetare da wadata al’umma da makamashi mai sauƙin kuɗi.
Sannan ya nuna aniyar kamfanin na haɗa kai da matatu masu zaman kansu da ya haɗa da haɗa kai da matatar ɗangote, duk a ƙoƙarin kamfanin na ganin an samar da wadatattun abubuwan da ake samu daga ɗanyen man fetur wanda zai zama mai sauƙi abin dogaro.
Haka zalika ya ba da tabbaci ga masu ruwa da tsaki cewa, kamfanin na ƙoƙarin daidaita matsalar musayar kuɗi ta hanyar ɗabbaƙa cinikayyar man ɗanyen man fetur da Naira wanda hakan zai rage amfani da kuɗin ƙasashen waje da kuma tamaka wa Nijeriya wajen faɗaɗa harkokin tattalin arziƙinta.
“Kun san matsalar makamashi na buƙatar musayar tunani, da ta ilimi da kuma aiki tare. Don haka ku zo mu haɗa kai wajen samar wa da Nijeriya makashi mai ɗorewa kuma mai sauƙi ga kowa da kowa,” in ji Mele Kyari a lokacin da yake jaddada buƙatar sabunta tunani da haɗin kai a fannin makamashi.
Daga ƙarshe ya yaba wa shugaba Bola Tiubu kan daidaita lamarin canjin kuɗi ta hanyar rage shigo da man da ake daga waje da ƙarfafa wa matatun man cikin gida guiwa wanda ya bayyana hakan a matsayin wata haɓɓasawa ta aiwatar da burin da kamfanin NNPC ke da ita na samar wa da Nijeriya tsayayyen makamashi.
