Raudhatur-Rasul za ta yi bikin cika shekaru 16 da kafuwa da karrama zakarun Gasar Ma’aiki

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Ƙungiyar Raudhatur-Rasul za ta yi bikini cika shekara 16 da kafawa, da karrama zakarun gasar musabaƙar yabon Ma’aiki (SAW) gami da karrarama muhimman mutane.

Za a gudanar da bikin ne a gidan Mumbayya, a ranar Lahadi da misalin ƙarfe 10:00 na safe.

Bilyaminu Zakariyya da aka fi sani da Abul-waraƙat Ayagi, shi ne shugaban ƙungiyar inda ya ce taron zai zama na musammam domin za a baje-kolin tarihi da ayyukan da ƙungiyar ta yi na shekaru 16, da kuma karɓar shawarwarin inganta ta.

“Taro ne na godiya ga Allah, da a cikin huwacewarSa Ya sa wannan ƙungiya ta cika shekaru 16 da kafawa, da tarin nasarori da ayyuka, waɗanda muka ƙididdige nau’o’in ayyuka 38 da muka yi. Wasu suka maimatu, wasu sau uku, biyar, bakwai zuwa sama, muka kuma ƙididdige ayyuka 135 da muka yi cikin waɗannan shekaru.

“Abu na biyu da taron zai ƙunsa, akwai musabakar sha’iran Jihar Kano da muka ƙirƙira, domin tsaftace harshe da alƙalami a yabon Annabi SAW. A karo na farko Mai Martaba Sarkin Kano ya halarta ya bada kyaututtuka ga zakarun.

Ya kara da cewa, “Shi wannan taron sha-kundum ne, domin zai haɗiye duk tarurrukanmu na baya.”

“A da mukan yi taro a mataki na unguwa, ƙaramar hukuma da ma na jihar, amma wannan duk ya fi su girma, sannan akwai manyan mutane masu mukamai, da malamai da shehunnai da sha’irai da manyan ƴan siyasa da kuma ma’aikata”, inji Ayagi.

By Babaji