Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Zaɓen kansilolin ƙananan hukumomin da ke gudana yau a Jihar Zamfara an samu ƙarancin fitowar masu kaɗa ƙuri’a a Gusau babban birnin jihar.
Matsalar ta faru ne yayin da aka samu jinkirin rarraba kayan zaɓe a sassa daban-daban na mazaɓu a babban birnin jihar.
Wakilinmu ya ruwaito cewa wasu daga cikin rumfunan zaɓe da aka ziyarta ba kowa, yayin da jama’a suka fita harkokinsu na yau da kullum.
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar ZASIEC ta shirya da ƙarfe 8:00 na safe domin fara zaɓen amma har rumfar zaɓe da gwamna Dauda Lawal ya kaɗa ƙuri’a ’a, kayan zaɓe da tantance masu kaɗa ƙuri’a bai fara ba sai da misalin ƙarfe 11:00 na safe.
Rahotanni sun bayyana cewa, jinkirin raba kayayyakin zaɓen ya shafi sauran ƙananan hukumomi 13 da suka rage a faɗin jihar.
Wakilinmu ya ruwaito cewa jam’iyyun siyasa 11 ne suka shiga zaɓen ban da jam’iyyar All Progressives Congress APC.
Jam’iyyar All Progressives Congress APC ba ta shiga zaɓen ba sakamakon ƙarar da jam’iyyar ta shigar na ƙalubalantar zaɓen a gaban babbar kotun tarayya da ke Gusau inda kotun tayi watsi da ƙarar kwanaki biyu da suka gabata kafin zaɓen.
A zantawarsa da wakilinmu, ɗaya daga cikin waɗanda suka kaɗa ƙuri’a mai suna Malam Yusuf Muhammad ya bayyana jinkirin kawo kayan zaɓen da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar ZASIEC ta yi a matsayin abin takaici.
A cewarsa, jinkirin bai rasa nasaba da yadda jam’iyya mai mulki a Jihar watau PDP ta ɗauki aniyar lashe zaɓen a jihar.
A hirarsa da manema labarai jim kaɗan bayan kaɗa ƙuri’a ’ar gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana zaɓen da aka gudanar a matsayin anyi shi cikin lumana.
Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa jam’iyyar PDP ce za ta lashe zaɓen a jihar.
“In sha Allahu jam’iyyar mu ta PDP za ta lashe dukkan zaɓukan da za a gudanar a faɗin ƙananan hukumomi 14 da muke da su a Zamfara duba da cewa ita ce jam’iyya ɗaya tilo da za ta iya ceto al’ummarmu daga halin da suke ciki na ƙuncin tattalin arziki”.
