Daga MUKHTAR A. HALLIRU TAMBUWAL a Sakkwato
Majalisar Sarkin Musulmi tare da haɗin Gwiwar Majalisar Haɗin Kan Matasan Musulmi ta Kasa (NACOMYO) reshen Jihar Sokoto da wasu ƙungiyoyin addinin Musulunci, sun gabatar da Taron Makon Tunawa da Gudunmawar Shehu Usmanu ɗanfodiyo karo na 11, da nufin tunawa da ayyukan ilimantarwa da yaɗa saƙon addinin Musulunci, da kuma adana su domin matasa masu tasowa.
Shugaban taron na bana Dr. Yayale Ahmad (Ajiyan Katagum), wanda ya taɓa riƙe muƙamin Sakataren Gwamnatin Tarayya, da wasu manyan baƙi da suka halarci wannan taron na bana sun bayyana muhimmancin ƙara ilimantar da al’ummar musulmi da faɗakar da su ƙalubalen da ke gabansu a wannan zamani, kamar yadda Shehu Usmanu ya gudanar a lokacin rayuwarsa.
Babban baƙo mai jawabi Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, OON, tsohon Ministan Sadarwa da Fasahar Zamani, ya gabatar da lacca mai taken, “Haɗin Kai A Matsayin Babbar Hanyar Samar Da Zaman Lafiya Da Kawar Da Talauci Da Fatara.”
Taron ya samu halartar Gwamnoni da wakilansu na jihohin Sakkwato, Kebbi, Katsina da sauransu. Har da tsofaffin gwamnonin jihohin Sakkwato, Jigawa da Kebbi, da wasu manyan malamai, sarakuna, ‘yan kasuwa, ‘yan siyasa. Akwai kuma baƙi daga ƙasashen Kamaru da Nijar, da su ma suka samu halarta.
An gudanar da laccoci a game da ɓangarorin ilimi da rayuwa daban-daban, da suka haɗa har da kacici-kacici a tsakanin ɗalibai daga makarantun sakandire da ke Jihar Sakkwato. An kuma gabatar da Daura ga matasa da mutanen masu buƙata ta musamman, tare da bita game da wasu littattafan Shehu ɗanfodiyo da sauran ɗalibansa, domin jawo hankalin al’umma game da muhimmancin ilimin da suke koyarwa, da kuma jihadin da waɗannan bayin Allah suka gudanar kafin, yayin da bayan Jihadin Shehu Usmanu ɗanfodiyo.
Daga ƙarshe Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya gabatar da kyaututtuka na karramawa da aka saba bayarwa duk shekara ga wasu zaɓaɓɓun mutane guda 5, wanda a ciki aka sanar da naɗin Babban Malamin Addinin Musulunci, kuma tsohon minista Farfesa Isa Ali Pantami, sarautar Majidaɗin Daular Usmaniyya.
