Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Matatar mai ta Ɗangote ta yi tayin samar da lita miliyan 60 na man fetur ga ƙungiyar Dillalan Man Fetur mai zaman kanta ta Nijeriya a duk mako, wanda ke nufin lita miliyan 240 a kowane wata.
Wannan jarida ta tattaro daga ƙungiyar cewa matatar ta amince da bai wa ‘yan ƙungiyar IPMAN lita miliyan 60 na fetur a mako-mako, ya danganta da irin tallafin da ake samu.
Hakan ya zo ne yayin da aka tattaro cewa matatar mai da ke Lekki ta dala biliyan 20 na da nufin tara biliyoyin daloli don shigo da ɗanyen mai da kuma ƙara yawan haƙo da mai a Nijeriya.
Har ila yau, a ranar Lahadin da ta gabata, dillalan man fetur sun bayyana cewa farashin man fetur ya ragu bayan man ya fara wadata, musamman yadda kamfanin man fetur na Nijeriya da sauran ‘yan kasuwa suka shigo da sama da lita biliyan biyu na fetur a cikin kwanaki 42.
A hirarsa da manema labarai, sakataren yaɗa labarai na ƙungiyar IPMAN, Chinedu Ukadike, ya ce mambobin ƙungiyar za su iya ɗaukar duk yawan adadin mai da matatar Dangote ta ware musu, yana mai jaddada cewa ’yan kasuwa masu zaman kansu ne ke ɗaukar mafi yawan man da ake shigo da su a cikin ƙasar.
Idan ba a manta ba, a baya-bayan nan ne ƙungiyar ta bayyana cewa ta ƙulla yarjejeniya da Dangote na fara jigilar mai kai tsaye daga matatar man ba tare da wani mai shiga tsakani ba.
