Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Tsohon shugaban ƙasa Cif Olusegun Obasanjo ya ce gazawar gwamnatin Nijeriya a ƙarƙashin mulkin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu “tabbas ce kuma a bayyane ta ke ga kowane mai son gaskiya ya gani.”
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Kehinde Akinyemi ya fitar, inda ta ce Obasanjo ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a taron shugabannin Chinua Achebe da aka gudanar a Jami’ar Yale, New Haɓen, Connecticut, Amurka.
“Kamar yadda duniya ke gani, halin da Nijeriya ke ciki ya yi ƙamari,” in ji Obasanjo.
Da yake magana game da gwamnatin Tinubu, ya ƙara da cewa, “Matsalar Nijeriya ta fito fili, inda kowa a duniya na gani.”
A cewar sanarwar, tsohon shugaban ƙasar a cikin jawabinsa mai taken ‘Rashin Jagoranci Nagari A Nijeriya’ ya ce, “idan al’ummar ƙasa ta yi rashin ɗa’a da cin hanci da rashawa, to ƙasar na ƙara tsunduma cikin ruɗani, rashin tsaro, rikici, saɓani, rarrabuwar kawuna, baƙin ciki, tawayar matasa, tashin hankali, da rashin ci gaba.”
“Halin da Nijeriya ke ciki: Kamar yadda muke iya gani da fahimta, abin ya yi ƙamari. Yawan fasiƙanci da fasadi na ƙara ƙaruwa, al’umma na ƙara shiga cikin ruɗani, rashin tsaro, da rikici, da saɓani da juna, rarrabuwar kawuna, da rashin haɗin kai.
“Wannan shi ne abin da ya fi yawa a Nijeriya a zamanin mulkin Baba-go-slow da Emilokan.”
Obasanjo a lokacin da yake magana a kan wasu littafai da aka buga a shekarar 1983, mai suna ‘The Trouble with Nigeria’ na Chinua Achebe ya ce, “Matsalar da Njjeriya ke fuskanta a zahiri gazawar shugabanci ce.
