Cibiyar bincike da ƙere-ƙere ta Jami’ar NSUK ta yi taron bajekolin 2024

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Cibiyar bincike na musamman da ƙere-ƙere da kuma kasuwanci wato Directorate of Research, Innovation and Enterprise COAAPBAS a Turance na babbar jami’ar jihar Nasarawa ta gudanar da babban taron bajekolin kayayyakin bincikenta karo na 8.

Babban taron wadda ake gudanar a jami’ar shekara-shekara an gudanar da na bana shekarar 2024 ne a jami’ar dake garin Keffi a makon da ake ciki.

Da take jawabi a matsayin ta na babbar mai makokin baki Shugabar Jami’ar Farfesa Sa’adatu Hassan Liman ta bayyana muhimmancin taron wadda ta ce yana bai da damar nuna basirar masu bincike wajen bunƙasar tattalin arzikin jihar dama ƙasa baki ɗaya.

Ta ce taken taron na bana ya dace matuƙa idan aka yi la’akari da buƙatar haɗin kai da aiki tare don cimma burin shirin.

Shugabar jami’ar Farfesa Sa’datu Hassan Liman ta kuma bayyana wasu nasarori da jami’ar ta cimma ta cibiyar binciken na musamman da ƙere-ƙere jami’ar da hakan ta ce ya jawo ra’ayin hukumomin tarayya suka kafa ƙarin ire-iren cibiyar a jami’ar tareda yaba wa gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule dangane da tallafi da yake bai wa jami’ar akai-akai musamman ta fannin inganta binciken.

Daga nan sai Farfesa Sa’adatu Hassan Liman ta yi kira na musamman ga al’umma baki ɗaya su yi na’am da sabon tsarin binciken na musamman don inganta da bunƙasa tattalin arzikin ƙasa baki ɗaya.

Tun farko a jawabinsa na maraba daraktan cibiyar binciken na musamman a jami’ar Farfesa Yakubu Boyi Ngwar ya bayyana cewa a bana cibiyar ta mayar da hankali ne wajen wayar da kawunan al’umma game da mahimmancin bincike da ƙere-ƙere don inganta tare da bunƙasa tattalin arziki.

Ya ce dole ne a riƙa aiwatar da basirar ƙere-ƙeren zamani don magance wasu ƙalubalen rayuwa da suka addabi al’umma a yanzu inda a ƙarshe ya yaba wa Shugabar Jami’ar Farfesa Sa’adatu Hassan Liman dangane da kyakkyawar tsari da take kawo jami’ar ta cibiyar binciken.

Sauran manyan baƙi da suka yi jawabi a wajen taron ciki har da wanda ya wakilci gwamnan jihar duk sun yaba wa hangen nesan Farfesa Sa’adatu Hassan Liman ta cibiyar inda suka ce tabbas an samu gagaruman cigaba a tattalin arzikin jihar da ƙasa ta cibiyar kawo yanzu.

Daga bisani an zagaya da manyan baƙin inda suka duba ire-iren kayayyakin binciken da aka bajekolinsu tare da bai wa wasu lambobin yabo na musamman da gabatar da lacca da sauransu.

By ukarofi