Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya buƙaci shugabannin Arewa a ranar Talata da su tashi tsaye wajen nemo hanyoyin da za su warware matsalolin da ke damun yankin.
Tinubu wanda mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya wakilta a yayin wani taron tattaunawa kan bunƙasa rayuwar matasan Arewacin Nijeriya wadda gidauniyar tunawa da Sir Ahmadu Bello ta shirya, ya ce akwai buƙatar shugabanni su tashi tsaye domin nema wa yankin mafita.
Taron dai an yi masa take da: ‘Tallafawa ba baya: dabaru masu ɗorewa wajen bunƙasa rayuwar matasan Arewacin Nijeriya’.
Ya ce abubuwan akhairin da marigayi Sir Ahmadu Bello, ya yi wa Arewa ya fito da cewa cigaban Arewa muhimmin abu ne ga cigaban Nijeriya.
Shugaban ƙasa ya ce, “Nijeriya ba za ta samun cigaba ba har sai kowanne yanki na ƙasar nan ya samun cigaban da ya dace, domin duk abin da ya shafi wani yanki na koma baya, to koma baya ne ga ƙasar nan bakiɗaya.”
Ya ce, akwai buƙatar a matsayinsu na shugabanni su yi aiki da tunani wajen lalubo mafita ga matsalolin Nijeriya. Ya ce wannan abu ne da za su iya.
Ya ce haka ne ya sa, “muka ba wa hukumar kula da Almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta muhimmanci da kuma haɗa kai da saurna gwamnatoci a matakai daban-daban domin tabbatar da kowanne yaro ya samu ilimi mai inganci.”
“Wannan ta sa domin tabbatar da kowa ya samu romon dimokraɗiyya, muka bai wa ƙananan hukumomi ‘yancinsu domin tabbatar da sun samu kuɗinsu da kulaa da ilimin firamare.”
Shugaban ƙasa ya kuma ce, harkar gwamnati ta haɗin guiwa ce kuma akwai buƙatar al’umma su zama alƙalai ga shugabanninsu domin tabbatar da kowanne yaro ya samu damar da ya dace.
Shugaba Tinubu har’ila yau, ya buƙaci ‘yan Arewa, musamman matasa, da su zama masu juriya da aiki tukuru da ibada a kamar yadda marigayi Sardaunan Sakkwato yake.
Ya ce irin kuzari da fikira matasa ke nunawa ba kawai zai amfanar da Nijeriya ba ne har ma da jan ragamar yankin Afirka wajen buɗe sabon shafi na cigaba da ƙere-ƙere.
“Matakin da ya kamata mu dauke na gaggawa shi ne bunƙasa ilimin masu tasowa. Ko dai mu kula da su yanzu ko kuma nan gaba su durƙusar da mu”.
Shi ma mai alfarma sarkin musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, kuma shugaban majalisar harkokin addini ta Nijeriya ya ba wa sukkan gwamnatoci shawara kan su ƙara yawan abin da suke warewa ilimi a jihohinsu.
“Ya kamata mu duba yadda za mu taimaka wa ‘ya’yanmu da ke kan titi ta hanyar gina makaranta da kawo musu malamai masu inganci da kuma shigo da sarakuna cikin harkokin gwamnati a faɗin ƙasar nan,” inji Sarkin Musulmi.
Daga nan, ya yaba wa gwamantin tarayya saboda samar da hukumar kula da Almajirai da yaran da ba sa zuwa makaranta, inda ya bayyana hukumar a matsayin mai muhimmanci.
Haka shi ma shugaban gidauniyar cibiyar tunawa da Sir Ahmadu Bello, Muazu Babangida, ya ce an kafa cibiyar ne domin bunƙasa shugabanci na gari a faɗin Nijeriya.
“Sama da shekaru 15 kenan wannan cibiya ke aiki wajen cimma manufar da ta sa aka kafa ta na wanzar da cigaba mai ɗorewa a Nijeriya musamman a ɓangaren ilimi.”
Ya ce manufar shirya zaman tattaunawar shi ne lalabo hanyar mafita mai ɗorewa game da rayuwar matasa da matsalar ƙaruwar yaran da ba sa zuwa makaranta.
Daga nan ya shawarci gwamantin da ta ɗauki shawarwarun da aka bayar a wurin taron da muhimmanci domin samun cigaba a wannan yanki.
Sauran waɗanda suka samu halartar taron sun haɗa da tsofaffin gwamnoni da masu ci da shugabannin ƙungiyar tuntuɓa ta Arewa (ACF), da jagororin ƙungiyoyin matasa da sauran masu ruwa da tsaki.
