Takarar Musulmi da Musulmi: Ndume ya buƙaci Bwala ya nemi gafarar Shettima

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya shawarci Daniel Bwala da ya nemi gafarar mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima.

A ranar Alhamis ne shugaban ƙasa Bola Tinubu ya naɗa Daniel Bwala, tsohon mai magana da yawun yaƙin neman zaɓen Atiku a matsayin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa.

Dangane da yaƙin neman zaɓe kafin zaɓen 2023, Tinubu ya zaɓi Shettima a matsayin abokin takararsa.

Bayan haka, Bwala ya yi murabus daga naɗin nasa a matsayin ɗan jam’iyyar APC, inda ya bayyana cewa ba zai iya goyon bayan tikitin takarar Musulmi da Musulmi ba.

Bayan haka Bwala ya taɓa zama kakakin tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar a yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Ndume, a wata sanarwa a ranar Asabar, yayin da yake mayar da martani ga naɗin Bwala, ya buƙace shi da ya yi aiki kafaɗa da kafaɗa da Shettima wanda shi ma ɗan jihar Borno ne.

Ndume ya ce, “Ka nemi gafara daga mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, wanda naɗin da ya yi maka ya sa ka bar APC saboda shi Musulmi ne.

“Ka yi aiki tare da Mataimakin shugaban ƙasa a matsayin mataimaki na inganta ajandar sabunta fata na shugaban ƙasa Tinubu.”

Ya kuma ƙara da cewa, “Ya kamata ka koyi darasi daga Sunday Dare da Bayo Onanuga waɗanda aminai ne ga Tinubu waɗanda a kullum suke kare manufofin shugaban ƙasa ba tare da cin zarafi ko caccaka ba.”

Ndume ya ba da shawarar cewa, “Ya kamata ka kuma yi koyi da irin su Hadiza Bala-Usman da kuma mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, waɗanda ke kare da kuma tallata manufofin Tinubu waɗanda suka goyi bayan gaskiya.

Ndume ya ƙara yaba wa shugaban ƙasa bisa naɗa Bwala. Ya bayyana cewa, Tinubu ya nuna cewa shi shugaba ne mai kishin ƙasa ta hanyar naɗin Bwala.

“Ina so in yaba wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa naɗa Daniel Bwala a matsayin mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin sadarwa da yaɗa labarai.

“Wannan karimcin ya cancanci yabo sosai, musamman ganin irin rawar da Bwala ya taka a baya.

Ndume ya ce “Naɗin na Bwala wata alama ce da ba kasafai ake samun irinta ba na nuna kishin ƙasa a cikin shugabanci,” in ji Ndume.

By ukarofi