Odita-Janar ya bankaɗo badaƙalar tiriliyan N3.4 a wasu ma’aikatun Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Ofishin babban mai binciken kuɗi na tarayya (OauGF) ya bankaɗo badaƙalar kuɗi da suka kai Naira Tiriliyan 3.403 a wasu ma’aikatu da hukumomin gwamnati da dama.

Laifukan guda 28 suna ƙunshe ne a cikin rahoton tantance ayyuka na shekarar 2021 na rashin bin ƙa’ida da gazawar kula da Ma’aikatun Tarayya na shekarar kuɗi ta 2021, wanda aka gabatar da su ga Majalisar Dokoki ta ƙasa ta hanyar wasiƙar lamba AuGF/AR. 2021/02, mai kwanan wata 15 ga Oktoba 2024 wanda babban mai binciken kuɗi na tarayya, Shaakaa Kanyitor Chira ya sanya wa hannu.

Rahoton ya ce Naira tiriliyan 2.902 na kuɗin ya fito ne daga gazawar da hukumomin gwamnati takwas suka yi wajen dawo da kuɗaɗen shigar da gwamnati ke yi, inda kamfanin hada-hadar wutar lantarki na Nijeriya ya kasa ƙwato Naira tiriliyan 2.896 na kuɗaɗen.

A cikin wata wasiƙar da ya aike wa magatakardar majalisar, babban mai binciken kuɗi ya ce rashawa wani ɓangare ne na abin da ya kira “batutuwan da ba su dace ba” waɗanda suke nakasa harkokin cikin gida.

Ya ce, an jawo hankalin kwamitocin kula da harkokin gwamnati na Majalisar Dokokin kan kowanne daga cikin waɗannan batutuwa ta hanyar shawarwari da suka haɗa da sanya takunkumi da nufin daƙile ɓacewar kuɗaɗe. Hakanan, an bi da waɗannan batutuwa dalla-dalla a ƙarƙashin kowace hukuma.

By ukarofi