Ƙudirin haraji: ’Yan Majalisar Wakilai na Arewa za su kare muradun ƙasa – Hon. Doguwa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban ƙungiyar reshen Arewa a Majalisar Wakilai Alhassan Doguwa, ya ce ƙungiyar za ta ba da maradun ƙasa wajen yin la’akari da ƙudurorin gyara haraji guda huɗu.

Yayin da yake jawabi ga manema labarai a Abuja a ranar Litinin, Doguwa ya ba da tabbacin cewa ƙungiyar za ta yi nazari a kan ƙudirin a tsanake kafin amincewa da shj.

Idan dai za a iya tunawa, dukkanin gwamnonin jihohin ƙasar 36, sun buƙaci a janye ƙudurin, saboda buƙatar ƙara tuntubar juna da kuma shawarwarin jama’a.

Sai dai Doguwa ya ce ƙungiyar ba za ta yi gaggawar yanke hukunci ba, yana mai cewa za a tuntuɓi juna da neman shawarwarin da suka dace.

“Waɗannan ƙudurorin da aka gabatar a fili suna da alaƙa da tsarin tarayya na kasafin kuɗi kamar yadda ya shafi raba albarkatu, ga ƙungiyoyin tarayya da manyan cibiyoyin gwamnati.

“Saboda haka, mu yi taka tsantsan, mu yi nazari sosai kan ƙudirorin, sannan mu yi la’akari da nufin yin adalci ga jama’a da kuma yin adalci ga ƙudirin, domin samun maslahar jama’a da ƙasa baki ɗaya.

“Haƙiƙa ba za mu yi gaggawar zartar da waɗannan ƙudirorin ba domin kauce wa yin gaggawar da zai iya yin illa kan tattalin arzikinmu na ƙasa baki ɗaya ba.

By ukarofi