Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ministan Kuɗi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun ya ce shugaban ƙasa Bola Tinubu na tsara hanyar fitar da ɗimbin ‘yan Nijeriya daga aangin talauci.
Ya bayyana hakan ne a Bauchi a ranar Litinin, yayin bikin bɗde taron Majalisar Kuɗi da Tattalin Arziki na ƙasa na 2024, wanda ake kira NACOFED.
Edun ya ce shugaban ƙasar bai bar wata kafa ba domin ganin an samu sauƙin rayuwa ga ‘yan Nijeriya ta hanyar fito da tsare-tsaren da za su amfani kowa.
“Gwamnatin shugaban ƙasa Tinubu ta gaji kadarori da basussuka kuma babu waiwaye sai dai batun tsara hanyar sa ido da tsara tsare-tsare domin a fara daidaita tattalin arzikin ƙasa.
“Yana aiki tuƙuru don samun jari ta hannun masu zuba jari daga cikin gida da waje masu zuba jari kai tsaye don ƙara haɓaka tattalin arzikin Nijeriya, bunƙasa tattalin arziki, samar da ayyukan yi da kuma fitar da ɗimbin jama’a daga ƙangin talauci.
“Lokacin da ku ka yi ƙoƙarin duba inda muke a yanzu, a zahiri, ana aiwatar da manyan gyare-gyaren tattalin arziki.
“Ya dakatar da asarar kashe kashi biyar cikin ɗari na tattalin arzikin ƙasar nan a duk shekara wanda bai ƙara wani amfani ba sai ga wasu ‘yan tsiraru da ƙasashe makwabta da ke cin gajiyar abin da ke faruwa da tallafin man fetur da kuma wani abin da ke da alaƙa da shi a musayar kuɗaɗen waje.
“An tanadi fa’idojin ne ga ‘yan kaɗan kuma yawancin ‘yan Nijeriya ba su samun wani fa’ida daga waɗannan tsare-tsare.
“An cire su kuma asusun tarayya zai amfana daga ƙaruwar albarkatun zuwa tarayya, jihohi da ananan hukumomi kuma za a iya yin wasu abubuwa da yawa ta fuskar zuba jari ba kawai a kan ababen more rayuwa ba amma a ayyukan zamantakewa kamar ilimi da lafiya,” in ji shi.
Ministan ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa hanyar a bayyane take ga ‘yan kasuwa masu zaman kansu kuma ƙasar ta dawo cikin harkokin kasuwanci a kan hanyar samar da masana’antu bisa abubuwan da ke faruwa a ɓangaren tace man fetur.
