Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina.
Gwamna Dikko Raɗɗa ya ƙaddamar da fara aikin hanyar Shargalle zuwa
Ingawa, inda ya shaida cewa, shimfiɗa sabuwar kwalta za a yi ba gyare-gyare ba.
Ya bayyana aikin hanyar mai tsawon kilomita 39 zai ci kuɗi Naira biliyan 3.8 kuma ana sa ran nan da shekara ɗaya za a kammala aikin hanyar.
Gwamnan ya sanar da bada kashi arba’in na kuɗin aikin ga ɗan kwangilar.
Akan haka ne ya jawo hankalin al’ummar yankin da su sa idon akan yadda ake aikin hanyar da zarar kun ga hankalin ku bai kwanta da aikin ba ku sanar da Ni” Malam Dikko yace.
Da yake nasa jawabin kwamishinan ayyuka a jihar, Injiniya Sani Magaji ya ja hankalin ‘yan kwangilar da su bi yarjejeniya da akayi da su wajen tafiyar da aikin domin samun ingantacciyar hanya.
Ɗan kwangilar Mr Maroon Ghostine ya tabbatar wa gwamna Dikko Raɗɗa cewa zasu kammala aikin hanyar kaman yadda aka yi yarjejeniya da su.
Kamfanin MotherCat aka ba kwataragin aikin hanyar da ta tashi daga Shargalle ta ɓulla Dutsi zuwa Ingawa.
Hanyar dai an gina ta ne shekara 45 da suka wuce lokacin mulkin Alhaji Balarabe Musa yana mulkin tsohuwar Jihar Kaduna.
