Da Ɗumi-Ɗumi: Kotun Ƙoli ta soke dokar caca ta Lottery

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Juma’a ne Kotun Ƙoli ta soke Dokar Caca ta Lottery da Majalisa ta samar a shekarar 2005.

Kotun, cikin wani hukunci da tawagar Alƙalai bakwai suka jagoranta, ta ce Majalisar ba ta da damar kafa doka game da lamuran da suka shafi Lottery da wasu nau’ukan caca.

Ta ce ire-iren waɗannan damanmakin majalisun dokokin jihohi kaɗai ke da alhakin kafa su.

Cikin hukuncin nata wanda Mai Shari’a, Mohammed Idris ya gabatar, kotun ta yi umarni cewa daga yanzu ba za a cigaba da yin aiki da dokar ba a duka jihohin Nijeriya sai dai ban da Abuja wadda Majalisa ta na damar kafa dokar a can.

An gudanar da shari’ar ne ƙarƙashin wata takardar ƙara da Jihar Legas tare da wasu jihohi suka shigar a shekarar 2008 kan ƙalubalantar Gwamnatin Tarayya game da gudanar da lamuran cacar Lottery.

By Babaji