Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aikawa Majalisar Dattijai wasiƙar neman tabbatar da naɗin Laftanar Janar Olufemi Olatubosun Oluyede a matsayin babban hafsan sojin Ƙasa na dindindin. A cikin wasiƙar da aka aika a ranar Juma’a, Shugaba Tinubu ya nemi majalisar ta tabbatar da naɗin Oluyede bisa tanadin Sashe na 218(2) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, tare da Sashe na 18(1) na dokar sojojin Nijeriya.
Oluyede ya soma aiki a matsayin muƙaddashin babban hafsan sojin Ƙasa a ranar 30 ga watan Oktoba, bayan rashin lafiyar Janar Taoreed Lagbaja, wanda daga bisani ya rasu a ranar 5 ga watan Nuwamba. Shugaba Tinubu ya bayyana ƙwarin gwiwarsa kan ingancin shugabancin, nagartar shi da kuma ƙwarewar Oluyede wajen jagorantar rundunar sojin kasar don tabbatar da tsaro da zaman lafiya.
Kafin wannan naɗin, Oluyede ya riƙe muƙamai da dama, ciki har da kasancewarsa kwamandan rundunar Infantry Corps ta Nijeriya a Jaji, Kaduna. An yi masa ƙarin girma zuwa Laftanar Janar a shekarar 2020. Oluyede ya kuma jagoranci ayyukan soja a wurare daban-daban, ciki har da aikin ECOMOG a Liberia, Operation HARMONY IV a Bakassi da Operation HAƊIN KAI a Arewa maso Gabas inda ya shugabanci 27 Task Force Brigade.
Janar Oluyede ya samu lambobin yabo da dama saboda ayyukansa na bajinta, ciki har da Corps Medal of Honour, Grand Service Star da Chief of Army Staff Commendation Award. Sauran sun haɗa da Field Command Medal da Field Training Medal. Oluyede, wanda aka naɗa a matsayin sojan a shekarar 1992 ya kasance jarumi mai nagarta a fagen soja. Yana da aure da yara uku.
