Lakurawa: Yadda sojoji ke aikin murƙushe ’yan ta’adda

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar, ya ce sojoji suna aiki tukuru don murkushe ayyukan Lakurawa da sauran ’yan ta’adda da ke addabar yankin Arewa.

Ministan wanda ya kai ziyarar aiki tare da duba kayayyakin yakin jirage na rundunar Operation Fansan Yamma, a Jihar Sakkwato ranar Litinin, ya ce sojoji sun ɗauki wani ƙwaƙƙwaran mataki kan Lakurawa.

Ya ce, “Kun ji daga bakin shugaban ƙaramar hukumar da Lakurawa suka kai wa hari a Jihar Kebbi, yana bayyana yadda sojoji suka mamaye yankin suka fatattaki Lakurawa.

“Hakan ya faru ne sakamakon jajircewa da jami’an tsaronmu suke yi,” a cewar ministan tsaron.

Ya ci gaba da cewa mutanen yankunan da abin ya shafa ne suka fi kowa bakin da za su yi magana aikin sojoji, domin su ganau ne a kan farmakin da sojoji ke kai wa mayaƙan.

“Mun ƙaddamar da wani sabbin makamai a Katsina tare da ƙaddamar da sabbin jiragen yaƙi masu saukar ungulu domin ragargazar ’yan fashin daji da da kuma Lakurawa, kuma za mu sake tura wasunsu zuwa Sakkwato,” in ji ministan.

Ya kai wa sojojin ziyara ne tare da Babban Hafsan Sojin Sama, Iya Mashal Hasan Bala Abubakar da wasu manyan hafsoshin soji.

By ukarofi