Majalisar malaman Musulunci ta nemi a dakatar da ƙudurin harajin Tinubu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Batun yi wa harajin Nijeriya garambawul da shugaban ƙasar Bola Tinubu ya aika wa majalisa na ci gaba da tayar da ƙura a ƙasar, inda a wannan karon, majalisar malaman addinin Musulunci ta Ulama Forum ta bayyana rashin amincewarta da ƙudurin, tare da yin kira da a dakatar da aiwatar da shi.

A farkon watan Oktoba ne Shugaba Tinubu ya ƙuduri aniyar yin wasu gyare-gyare a tsarin karɓar haraji, ciki har da harajin ɓAT da sauransu, lamarin da ya sa gwamnatin tarayya da gwamnonin arewa suka sa zare, har gwamnonin suka buƙaci a dakatar da aiwatar da ƙudurin.

Haka kuma majalisar tattalin arzikin ƙasar da wasu ‘yan majalisa sun nuna rashin amincewarsu da ƙudurorin, amma duk da haka, Shugaba Tinubu ya ce yana kan bakarsa ta aiwatar da gyare-gyaren, tare da kira da a bar majalisa ta yi aikinta.

A wata sanarwa da majalisar malaman ta fitar a ranar Litinin, wadda shugabanta, Aminu Inuwa Muhammad da sakatarenta injiniya Basheer Adamu Aliyu da sauran malamai suka sanya wa hannu, sun bayyana cewa a sabon tsarin, mafi yawan kuɗaɗen haraji da za a riƙa tarawa, wasu tsirarun jihohi ne za su fi cin moriya.

“Kudurin gyara haraji na Tax Reform Bills, musamman na Nigeria Tax Bill (NTB), 2024 da na Nigeria Tax Administration Bill (NTAB) 2024 babu daidaito a ciki,” in ji sanarwar.

“ƙudurin NTAB zai sa a riƙa kwashe mafi yawan harajin VAT da aka tara a jihohi zuwa jihohin da shalkwatar kamfanonin suke. Wannan tsarin ya saɓa ƙa’idar samar da daidaito, domin duk kayayyakin da kamfani ke yi, ba su da amfani matuƙar babu masu amfani da su.

“Babu adalci a ciki saboda masu biyan harajin ba za su ci moriyar kuɗaɗen da suke biya ba, wanda hakan ya saɓa da ƙa’idar karɓar haraji kamar yadda yake a ƙunshe a cikin kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999.

“Sannan a sabon tsarin na NTB, za a rufe wasu muhimman ɓangarorin gwamnati kamar TETFUND da NITDA, wanda su ne ke taimakawa wajen samar da ababen more rayuwa da tallafin karatu.”

Majalisar malaman ta kuma zayyano wasu abubuwa da ta ce ta gano suna ƙunshe a cikin ƙudurorin, waɗanda a cewarta suka sa ta yi fatali da gyare-gyaren.

“ƙudurin na NTB 2024 da na NTAB 2024, za su tattara wasu haraji masu kusanci su zama ɗaya. Sai dai matsalar ita ce, jihohin da shalkwatar kamfanonin suke, su ne za su fi cin moriyar kuɗaɗen da aka tara, maimakon jihohin da masu amfani da kayayyakin suke.

“ƙudurorin za su fi amfanar jihohi uku, sama da sauran jihohin ƙasar, wanda hakan zai shafi tattalin arzikinsu.”

Majalisar ta ƙara da cewa ɓullo da garambawul ɗin a wannan lokacin da ake fama da tsadar rayuwa a Nijeriya ba daidai ba ne, sannan ta ƙara da cewa ƙudurin NTB zai sa a rage kuɗaɗen da ake bai wa asusun tallafa wa ilimi na TETFUND da NITDA da NASANI maimakon kashi 4 na ribar kamfanonin a 2025 da 2026 zuwa kashi 2 a 2030.

“Idan aka hana hukumomin samun kuɗaɗe da suke samu daga asusun deɓelopment leɓy, da wahala su cigaba da aiki ko da kuwa suna samun kuɗi daga gwamnatin tarayya,” in ji majalisar malaman, sannan suka ƙara da cewa hakan zai shafi harkokin TETFUND sosai.

“Wannan zai so dole makarantun su nemi wasu hanyoyin samun kuɗaɗe domin inganta makarantu da bincike-bincike da ɗaukar nauyin malamai domin ƙaro karatu da sanin makamar aiki, wanda hakan zai sa dole makarantun su ƙara kuɗin makaranta.”

Malaman sun kuma bayyana cewa sun yi nazarin ƙudurorin da abubuwan da za su biyo baya, musamman ga jihohin da suke zargin za a danne, inda suka ce lallai akwai buƙatar gwamnatin tarayya ta saurari buƙatar majalisar tattalin arzikin ƙasar.

“Wannan zai sa a fahimci juna sannan su dace da dokokin ƙasar tare da wanke zargin cewa bankin duniya da bankin bada lamuni ne suka ƙaƙaba wa Nijeriya su,” in ji sanarwar majalisar, sannan ta bayar da shawarwari kamar haka:

Ya kamata gwamnoni su nemi shawarwari daga masana domin a yi nazarin ƙudurorin sosai.

Gwamnonin su buƙaci a dakatar da aiwatar da ƙudurorin a yadda suke a yanzu ba tare da an yi gyara ba.

A bayar da damar nazari tare da muhawara a kan ƙudurori.

‘Yan majalisar dokoki su yi abin da ya kamata wajen ƙin amincewa da ƙudurorin da za su cutar da waɗanda suke wakilta

Dukkan ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun mutane su fito bayyana rashin amincewarsu da tsarin.

A ƙarshe majalisar malaman ta Ulama Forum ta ce, “muna kira da a janye ƙudurorin, a koma teburin tattaunawa domin a samu matsaya mai kyau.”

By ukarofi