Asibitin Albarka zai gudanar da duba lafiyar haƙoran mutum 300 kyauta a ƙaramar Hukumar  Dala

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An yaba wa Asibitin Albarka ƙarƙashin Dakta Muhammad N. Salihu  bisa ƙoƙarin da suke yi na taimakon al’umma marasa ƙarfi, ta ɗaukar nauyin kula da lafiya a tsakanin al’umma kyauta a ɓangarorin lafiya daban-daban. 

Shugaban ƙaramar Hukumar Dala, Alhaji Surajo Ibrahim Imam ne ya yi yabon lokacin da tawagar jami’an asibitin suka kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa.

Alhaji Surajo Imam ya ce shugaban Asibitin Albarka, Dakta Muhammad Nuhu Salihu tun yana matsayin daraktan kula da lafiya a asibitin ƙashi na Dala yake tallafa wa al’ummar yankin.

Ya kuma ba shi tabbacin yin haɗin gwiwa mai ƙarfi tsakanin ƙaramar hukumar Dala da Asibitin Albarka wajen inganta harkokin kiwon lafiya ga mazauna Dala.

Dakta Muhammad N. Salihu, shugaban Asibitin na Albarka ya bayyana cewa ziyarar da suka kai ƙaramar hukumar Dala ta taya Alhaji Surajo Imam murnar zaɓen da aka yi masa da rantsar da shi a matsayin shugaban  ƙaramar hukumar ne.  

Ya kuma tabbatar wa shugaban na Dala Asibitin Albarka zai himmatu wajen tallafawa gwamnatinsa domin bada gudunmuwa wajen inganta lafiya.

Sannan ya sanar da wani shiri da asibitin Albarka zai gudanar na aikin tsaftace haƙora da dasa haƙora kyauta ga mazauna ƙaramar hukumar Dala 300.

Dakta Muhammad N. Salihu ya ce duba lafiyar haƙoran zai shafi masu ƙaramin karfi ne, an  kuma tsara shirin za a yi nan da ƙarshen wannan shekara ko kuma a farkon watannin sabuwar shekara mai zuwa.

Da yake bayani kan haƙora masanin ilimin haƙora Malam Kabiru Dalha ya bayyana rashin wayar da kan al’umma kan tsaftar haƙori na daga cikin abinda ya sa mutanen ke sakaci da hakan kan iya yin illa ga lafiyarsu, shiri na kula da haƙora da wayar da kan jama’a zai taimaka wajen magance waɗannan matsaloli.

By ukarofi