Korarren mataimakin shugaban UNIZIK ba ma’aikacinmu ba ne – Jami’ar Gusau

Spread the love

Daga ADAM MUHAMMAD a Gusau

Jami’ar Tarayya ta Gusau da ke Jihar Zamfara ta kori batun da ke cewa korarren Shugaban Jami’ar Nnamdi Azikwe (UNIZIK) ta Jihar Anambra, Dokta Bernard Ifeanyi Odoh ma’aikacinta ne, inda ta ce bai taɓa aiki a matsayin ma’aikacin Jami’ar ba.

Shugaban jami’ar ta Gusau, Farfesa Mu’azu Abubakar ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Gusau.

Ya ce ikirarin da Dakta Odoh ya yi na cewa ya samu matsayin kaiwa Farfesa a Jami’ar ta Gusau (FUG) soki-burutsu ne .

Farfesa Muazu Abubakar ya ce, Daktan bai ya aiki a jami’ar ba kuma ba a naɗa shi a matsayin farfesa ba.

Ya kuma ce, wasiƙun da ake kira wasiƙun bayar da wa’adin zama Farfesa da kuma tabbatar da matsayin Farfesa, mai kwanan wata 30 ga Afrilun 2015 da 12 ga Nuwamban 2015, wanda Dakta Odoh ya gabatar da su, sun kasance na zamba da ƙarya tsagwaron ta.

Ya ce wasiƙun da ake kira wasiƙu da ba da naɗin mukamai da ake zargin cewa an tabbatar da kwafin gaskiya ne wanda tsohon magatakardar jami’ar, Ibrahim Bawa Ƙaura ya amince da shi a ranar 8 ga Nuwamba, 2024, shekaru shida bayan ya bar aikin jami’ar, samfurori ne na damfara da Dakta Odoh ya shirya, tare da haɗa baki da tsohon magatakardan Jami’ar don ɓata mata suna a idon Duniya.

“A game da Dokta Odoh Bernard Ifeanyi, Jami’ar ta lura kamar haka: bayan amincewa ya zamo malami bai gabatar da wata takarda ta amincewa da tayin ɗaukar shi aiki ba, hakazalika bai taɓa ziyartar Sashen Nazarin Geology na Jami’ar ba don ya koyar da ɗalibai duk da cewar albashin ya fara zuwa daga watan Yuli 2014 zuwa Agusta 2015″, Inji Farfesa Mua’azu.

Farfesa Mua’azu Abubakar ya ce duk abin da aka ce Dakta Odoh ya yi na naɗa shi a matsayin ma’aikaci da kuma tabbatar da ƙarin girma a matsayin farfesa bai dace ba, zamba ne, ba tare da bin ƙa’ida ba da kuma zangon-ƙasa.

Ya jaddada cewa babu wata shaida da ta nuna a hukumance dangane da batun daukarsa a matsayin ma’aikacin Jami’ar Tarayya ta Gusau.

“Duk wani ikirari akasin haka da Dakta Odoh ya yi, ba komai ba ne illa ɓata sunan Jami’ar don ya zamo Shugaban Jami’ar Nnamdi Azikiwe University dake Awka, ta hanyar bayar da takardardun bogi”, inji Farfesa Abubakar.

Farfesa Mua’azu ya bayyana cewa, hukumar gudanarwar Jami’ar za ta ɗauki mataki na gaba kan tsohon magatakardar Jami’ar Ibrahim Bawa da kuma Dakta Efeanyi Bernard Odoh domin kare mutuncin Jami’ar.

By Babaji