Shettima ya wakilci Tinubu wajen buɗe wasannin sojojin Afirka karo na biyu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga sojoji a sassan Afirka da su haɗe kai don magance matsalolin tsaro da suka zama barazana ga haɗin-kai acikin al’ummar Nahiyar.

Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a yayin buɗe wasannin sojojin Afirka karo na biyu, a Abuja.

Ya ce, taron wani fage ne na kafa tarihi da kuma ƙarfafa alaƙa tsakanin sojoji a Nahiyar.

Taken wasannin shi ne ‘Enhancing Military Cooperation in Afrika through Sports’, wato bunƙasa haɗin-kai tsakanin sojojin Afirka ta hanyar wasanni, wanda aka fara shi tun sama da shekaru 20 da suka gabata.

Shugaba Tinubu, wanda Mataimakinsa, Kashim Shettima ya wakilce shi, ya ce babu wata ƙasa da za ta iya magance matsalolin tsaro da ke addabar ta ba tare da agaji daga waje ba, ya na mai nuni da muhimmanci haɗin kai wajen yaƙar ta’addanci.

A lokacin da ya ke magana game da shirin, Shugaba Tinubu ya yaba wa Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa da shugaban shirya wasannin, Manjo-Janar M. Abdullahi kan jagorancinsu ga lamuran wasannin.

Ya kuma bayyana yadda wasannin ke ƙara kuzari da horo musamman acikin jami’an sojoji wanda hakan zai taimaka wa ƙoƙarinsu na daƙile ayyukan ta’addanci.

By Babaji