Yahaya Bello ya sake miƙa kansa ga EFCC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Alamu masu ƙarfi sun nuna cewa tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya sake amsa gayyatar Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin ƙasa Ta’annati, EFCC kan zargin sauya akalar wasu kuɗaɗe.

Wata majiya daga hukumar ta bayyana wa manema labarai cewa a safiyar ranar Talata ne Yahaya Bello tare da lauyoyinsa suka halarci ofishin hukumar dake Abuja.

Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan da Kotun Ƙoli ta yi watsi da ƙarar da ke ƙalubalantar halascin EFCC.

A makon da ya gabata ne aka yi ta raɗeraɗin cewa tsohon gwamnan zai je ofishin hukumar a wani karon inda aka yi ta ƙoƙarin ji daga jami’an labaransa wanda hakan bai samu ba.

A ranar 14 ga watan Nuwamba ne EFCC ta nemi a ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 27 ga wata bayan shigar da wata sabuwar ƙara da hukumar ta yi.

By Babaji