Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano
Wasu shugabannin masana’antu da ke Kano sun yi kira da Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu da gwamnan Kano da sauran masu ruwa da tsaki kan su kawo tallafi na samar da ingantacciyar wutar lantarki domin bunƙasar masana’antu a Kano da Nijeriya baki ɗaya kamar dai yadda Alhaji Ado Sani Salt Lick, ya bayyana a lokacin taro nuna kayayyaki da masana’antu Kano ke sarrafawa da samarwa ga al’umma domin ci gaban jihar da ƙasa baki ɗaya.
Alhaji Ado Sani wanda jami’i ne mai kula da saye da siyarwa, ya yaba wa ƙungiyar masu masana’antu ta ƙasa reshen Jihar Kano ƙarƙashin shugabancin Alhaji Madugu, kan shirya wannan taro da ya ba damar fito da matsalolinsu, domin su sanar da gwamnati don ɗaukar matakai.
Shi ma Muhammad Tahir na masana’antar LEE GROUP bayyana yadda suke taimakawa ya yi wajen ɗaukar matasa aiki da kuma biyan haraji ga gwamnati kamar yadda yake a tsarin gudanarwa na kawo cigaban ƙasa.
Haka shi ma Muhammad Isah, Beatrice Ezeocho, dukkanin su jami’ai ne daga masana’antar Tofa G I, wanda suka ce a ɓangarensu, suna fitar da Afirka kunya tolifefa da makamantansu, wanda matasa kan samu aiki a dalilin hakan.
Abdulhamid Addau Hassan, haka shi ma Kannady Domino, dukkanin su, sun nemi a gajin gwamnati dan faɗaɗa sana’arsu da za ta cigaba da bunƙasa tattalin arziƙin Nijeriya
