Kocin Super Eagles, Austin Eguavon ya gayyaci ’yan Kano Pillars uku ciki har da Rabi’u Ali, domin karawa da Ghana a neman shiga gasar CHAN 2025.
Sauran da aka kira daga Pillars sun haɗa da Abiam Nelson da kuma Adams Aminu Sani a tawagar ta Super Eagles masu taka leda a gida.
Rabi’u Ali yana kan ganiya a wasannin firimiyar Nijeriya ta bana, wanda ya zura ƙwallo takwas a raga, bayan kammala wasannin mako na 15.
Ana sa ran ’yan wasan da aka gayyata za su je katafaren filin wasa na Remo Stars a Ikenne da ke jihar Ogun daga ranar 4 ga watan Disamba, domin karɓar horo.
Super Eagles za ta fara zuwa Ghana a wasan farko ranar 22 ga watan Disamba, sannan a buga fafatawa ta biyu ranar 28 ga watan Disamba a Godswill Akpabio Stadium a Uyo jihar Akwa Ibom.
Za a buga gasar CHAN 2025 ta ’yan wasan da ke taka leda a gida a cikin watan Fabrairun 2025 a Kenya da Uganda da kuma Tanzania.
Ghana ta yi wa Super Eagles fintinkau a zuwa gasar CHAN a 2009 da kuma 2023, inda Nijeriya ta zama ’yar kallo.
