Lampard ya zama sabon kocin Coventry City

Spread the love

An naɗa tsohon ɗan wasan tsakiya na ƙungiyar ƙwallon ƙafar Chelsea da ƙasar Ingila Frank Lampard ya zamo kocin Coventry a bisa yarjejeniyar shekaru 2 da rabi.

Lampard ya maye gurbin Mark Robins, wanda aka sallama a farkon wannan watan.

Coventry na mataki na 17 a gasar zakarun bayan wasanni 17 inda suka yi rashin nasara a wasanninsu 4 na karshe.

A matsayinsa na ɗan wasa, Lampard ya ciwa Chelsea ƙwallaye 211 a dukkanin gasar da ta buga a shekaru 13 da ya shafe a cikinta masu cike da daukar kofi.

Ya taɓa horar da ƙungiyoyin Chelsea da Everton a gasar firimiya, haka kuma ya horas da ƙungiyar Derby County.

Lampard zai karɓi ragamar horas da Coventry a karon farko ran Asabar mai zuwa inda za ta kara da ƙungiyar Cardiff City a filin wasa na Coventry Building Society.

By ukarofi