Daga MUAZU HARDAWA a Bauchi
Kungiyoyin ƙasa da ƙasa masu bayar da tallafi kan yaƙi da cututtuka da ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar Bauchi sun gudanar da bikin tunawa da ranar masu ɗauke da cutar SIDA a duniya na shekarar 2024 a Bauchi.
Dr Sani Mohammed Dambam kwamishinan kiwon lafiya na jihar Bauchi shi ne ya jagoranci bikin na bana yadda ya bayyana nasarori da aka samu wajen yaƙi da cutar.
Yadda cikin jawabinsa a wajen taron ranar ta masu ɗauke da cutar Mai karya garkuwar jiki HIV AIDS, wanda aka gudanar a dakin taro na Aliko Dangote College of Nursing Bauchi a yammacin litinin 2 ga December 2024, ya bayyana samun nasara a yaƙi da cutar a jihar Bauchi.
Majalisar Dinkin Duniya ta assasa kowace ranar 1 ga watan Disamba a matsayin ranar tunawa da masu ɗauke da cutar sida a duniya
Dr. Sani Mohammed Dambam ya bayyana samun nasara wajen yaƙi da cutar a jihar Bauchi saboda wayar da Kai da kuma daukar matakan kariya da bayar da maganin kyauta a cibiyoyi sama da 800 da ake bayarwa da kuma manyan cibiyoyi a kalla ana da guda ɗaya a kowace ƙaramar hukuma a jihar Bauchi.Ya buƙaci kowace mace mai ciki ta je asibiti a yi musu awu don gano matsayin su game da cutar.
Dr Yakubu Gida Abdullahi shi ne mai riƙe da hukumar Bacatma masu yaƙi da cutar HIV AIDS a jihar Bauchi Shima cikin jawabinsa a wajen Taron ya bayyana samun nasara a kan yaƙi da cutar sakamakon ƙarin likitoci da ƙungiyoyin da suke taimakawa wajen yaƙi da cutar.
