Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Jam’iyyar APC ta ƙaddamar da kwamitin sulhu mai mutum takwas domin gyara tsarin jam’iyyar da warware rikice-rikice a jihar Adamawa.
An bayyana wannan mataki ne a ranar Laraba a Yola, yayin wani taro da mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin Arewa maso Gabas, Mustapha Salihu ya jagoranta.
Sakataren yaɗa labarai na APC a Adamawa, Mohammed Abdullahi ya ce kwamitin na karkashin jagorancin Sanata Muhammed Mana.
Sanarwar da Manhaja ta samu ta bayyana cewa kwamitin ya ƙunshi wasu jiga-jigai kamar Sanatoci Bello Tukur, Abubakar Girei, Binta Garba da Injiniya Martins Babale.
Sauran ‘yan kwamitin sun haɗa da Hon. Yusuf Buba Yakubu, Dr. Bridget Zidon, da kuma Barista Isa Baba, wanda ke matsayin Sakataren kwamitin.
Aikin da aka ɗora wa kwamitin ya haɗa da warware matsalolin cikin gida, ƙarfafa haɗin kai tsakanin ’ya’yan jam’iyyar.
A yanzu haka dai kwamitin ya fara zama a Abuja kuma zai fara aikin sulhu kai tsaye a Adamawa nan ba da daɗewa ba.
Taron da APC ta gudanar a Yola ya samu halartar shugabannin zartarwar jam’iyya na jiha, shugabannin jam’iyya na ƙananan hukumomi da kuma ’yan majalisar dokokin jiha.
A yayin taron, APC ta jaddada cewa haɗin kai da fahimtar juna su ne mabuɗan nasarar jam’iyyar a zaɓukan gaba.
Jam’iyyar APC ta bayyana taron a matsayin ci gaba daga wani taron farko da aka yi a Abuja tare da mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Malam Nuhu Ribadu.
A wani rahoton, kun ji cewa rikicin APC ya ƙara ƙamari a jihar Benue yayin da wata kotu ta kori shugabannin riƙo da Abdullahi Ganduje ya naɗa.
An ruwaito cewa A ranar 21 ga watan Agusta, Ganduje ya naɗa shugabannin saboda rikicin shugabanci da jam’iyyar ke fama da shi.
