LAFIYA UWAR JIKI: Haɗarin istimna’i ga lafiyar jikin mutum (6)

Spread the love

Tare da MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI

Illarsa ga garkuwar jiki 

Yawan aikata wannan abu, wato auren hannu, ya na da illa ga garkuwar jikin ɗan adam.  Dabi’antuwa da istimna’i ya na sawa a tsarto wani sinadari da ake kira ‘cortisol’ a turance cikin jini. Da akwai wasu halittu na musamman da su ke akan kowacce ƙodar mutum ta hagu da ta dama, su ne ke da alhakin tsarto da wannan sinadari. A likitance, ana cewa da shi ‘sinadarin gajiya’.

Daga cikin aikinsa shi ne ƙara gudu da saurin yadda jiki ke gudanar da ayyukansa. A ƙa’ida, mafi yawan aikin da jiki zai yi, akwai buƙatar a ƙone wani makamashi, domin samar da kuzarin gudanar da wannan aiki, wato akwai buƙatar ‘energy’ kenan. 

Saboda haka yawan yin istimna’i zai sanya sinadarin kotisol ya yi yawa a cikin jini, wanda hakan zai bayu izuwa ƙaruwar wahala da aikin da jiki zai yi, hakan kuma zai sanya ƙwayoyin halittun jiki su yi saurin gajiya. Shi ya sa yawan yin zinar hannu ko istimna’i ke kawo gajiya da rashin kuzari, musamman ma su yi sau da yawa a kowacce rana.

To, idan ana samun yawan wannan sinadari akai-akai a cikin jini, hakan zai raunata garkuwar jikin ɗan adam ta yadda cuta ƙarama ma sai ta samu damar shiga jikin ba tare da wata wahala ba.

Kamar yadda na faɗa, za a samu yawan gajiya a jiki, wacce idan ta kai maƙura, za ta iya jawo wa ɗan adam saukowar tsufa da wuri (premature ageing). Allah ya kiyaye. 

Naku, Mustapha Ibrahim Abdullahi

©MIAbdullahi 2024

By ukarofi