Nijeriya za ta nemi bashin tiriliyan N13 don cike giɓin kasafin 2025 – Minista

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministan Kuɗi da Tattalin Arziƙi na Nijeriya, Wale Edun ya bayyana cewa gwamnatin ƙasar za ta nemi bashin naira tiriliyan 13 don cike giɓin da ke cikin kasafin kuɗin shekara mai zuwa.

A jawabin da ya gabatar gaban manema labarai bayan halartar taron majalisar tattalin arziƙi da ya gudana a fadar shugaban ƙasa ta ɓilla da ke Abuja, Mr Edun ya ce bashin ne kaɗai hanyar da Nijeriya za ta iya magance matsalar ta giɓin kasafin kuɗi a wannan karon.

Jimillar kuɗin gudanar da ayyuka da ke cikin kasafin ya kai naira tiriliyan 34 da biliyan 8 daga cikin ƙunshin kasafin na naira tiriliyan 47 da biliyan 9 wanda ke nuna ƙaruwar kashi 36.8 daga kasafin 2024.

Jimillar giɓin da ke ƙunshe a kasafin na bana na matsayin naira tiriliyan 13 da biliyan guda wato kashi 3.39 na ma’aunin tattalin arziƙi na GDP.

A cewar Mr Edun an gudanar da kasafin kuɗin na baɗi ne bisa ga duba ga irin gagarumin ci gaban da ƙasar ta samu ƙarƙashin jagorancin watanni 18 da Shugaba Tinubu ya shafe a kan kujerar mulkin ƙasar.

By ukarofi