Kirsimeti: Atiku ya yi kira a zauna lafiya da nuna ƙaunar juna

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Tsohon mataimakin shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su rungumi soyayya da haɗin kai, yana mai cewa lokaci na Kirsimeti ya kamata ya zama abin koyi wajen zaman lafiya da fahimtar juna.

Atiku ya bayyana haka ne cikin wani saƙo na musamman da ya fitar a Abuja, inda ya ja hankalin ‘yan ƙasa kan muhimmancin nuna tausayi da sadaukarwa domin cigaban al’umma.

A cikin saƙonsa, Atiku ya ce lokaci na Kirsimeti ya dace muyi tunani mai zurfi game da muhimmancin haɗin kai da zaman tare. Ya kuma yi kira ga shugabannin siyasa da su sanya muradun al’umma a gaba, tare da yin dukkan sadaukarwar da ake buƙata domin inganta rayuwar ‘yan Nijeriya. Ya bayyana cewa, ta hanyar haɗin kai da soyayya, duk wani ƙalubale zai iya zama mai sauƙi.

Atiku ya kuma yi fatan Kirsimeti mai albarka ga dukkan ‘yan Nijeriya, yana mai addu’ar zaman lafiya, farin ciki, da kuma fata na alheri ga makomar ƙasar.

Ya ce lokaci ne na soyayya da jin daɗi tare da kowa, tare da buƙatar kowa ya zama mai kyautatawa da kyakkyawan fata ga juna.

By ukarofi