Jam’iyyar NNPP ba ta rabe ba – Asiwaju Shittu

Spread the love

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Tsohon shugaban jam’iyyar Alliance National Party (ANP), Asiwaju Moshood Shittu, ya musanta raɗe-raɗin da ake yi cewa an samu rikici a cikin jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP).

Da yake magana yayin wani taron manema labarai a Abuja jiya, Shittu ya jaddada cewa, jam’iyyar NNPP ƙarƙashin jagorancin mai girma Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na nan dunƙulalliya, mai ƙarfi, kuma ita ce kaɗai jam’iyyar adawa mafi ƙarfi da za ta iya lashe kujerar shugaban Ƙasa a 2027.

Ya ƙara da cewa, jam’iyyar Alliance National Party (ANP) na daga cikin jam’iyyun da suka yi haɗaka da NNPP domin ta kara ƙarfi.”

Shittu ya bayyana cewa, ɓangaren da ake kira Anubonam na ƙoƙarin haddasa rarrabuwar kawuna da tayar da hankali. An san cewa wannan ɓangaren suna amfani da sunan jam’iyyar domin neman alfarma, kamar yadda aka yi zargi. Saboda haka, ana shawartar jama’a su yi taka-tsan-tsan da wannan makirci nasu.

Ya tunatar da cewa, INEC ta miƙa sabon tuta, kundin tsarin mulki da tambarin jam’iyyar NNPP a taron da aka gudanar a Otal din Bolingo da ke Abuja, inda dukkannin shugabannin NWC, NEC, da mambobi tare da jagororin jam’iyyar suka halarta.

Asiwaju Shittu ya yaba da jagorancin mai girma Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, yana cewa, irin jagorancin ƙwarai da Kwankwaso ke yi ne ya sa jam’iyyar NNPP ke ƙara samun ƙarfi a dukkan shiyyoyin siyasa guda shida na ƙasar nan.

A 2027, NNPP na da damar lashe kujerar shugaban Ƙasa, gwamnoni, sanatoci, ‘yan Majalisar Tarayya da na jihohi.

A ƙarshe, ya yi kira ga mambobin jam’iyyar da su yi watsi da salon wannan ɓangaren da aka kora, yana mai jaddada cewa, INEC ce kaɗai ke da hurumin tabbatar da ingancin kowace jam’iyya. Farkon Kwankwaso ne ya karɓi tuta, tambari da kundin tsarin mulki na jam’iyyar NNPP, wanda hakan ke nuna cewa jam’iyyar dunƙulalliya ce.”

Ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya masu neman jam’iyyar siyasa da su shiga NNPP domin samun damar shiga cikin tafiyar siyasa mai nagarta.

By ukarofi