Wasu mazauna Ibadan sun gudanar da zanga-zanga a kan hukuncin kotu na tsare tsohuwar matar Ooni, Naomi Ogunwusi, fitaccen mai gabatar da shirye-shirye Oriyomi Hamzat da shugaban makarantar Islamic High School bisa zargin su da hannu a turmutsutsun da ya yi sanadin mutuwar yara sama da 36. Wannan al’amari ya faru ne yayin wani taron bikin Kirsimeti na yara da aka gudanar a makarantar.
Kotun Majistare a Ibadan, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Olabisi Ogunkanmi, ta bada umarnin tsare su a gidan yari na Agodi har zuwa 13 ga Janairu, lokacin da za a sake sauraron shari’ar. ‘Yan sanda sun tuhumi waɗanda ake zargin da laifuffuka guda huɗu, ciki har da kisan kai, haɗa kai wajen aikata laifi, da sakaci wanda ya janyo asarar rayuka, bisa tanadin sashi na 324 na dokar laifuffuka ta jihar Oyo.
Mai gabatar da ƙara, Sufeto Sikiru Opaleye, ya bayyana cewa waɗanda ake zargin sun shirya wannan taron amma sun kasa samar da tsari mai kyau da matakan tsaro da kulawa da lafiya, lamarin da ya haifar da turereniya da ya yi sanadin mutuwar yara 35 da jikkatar wasu shida. Wannan ya hada da wata yarinya mai shekaru takwas da sauran yara ‘yan wata biyar zuwa shekaru 13.
Bayan hukuncin, wasu mazauna sun yi zanga-zanga suna kira da a saki Oriyomi Hamzat, suna cewa yana ƙoƙarin taimako ne kawai. Haka zalika, tsohuwar matar Ooni, Naomi Silekunola, wadda ta jagoranci shirya taron ƙarƙashin gidauniyarta mai suna WINGS, ita ma tana daga cikin waɗanda ake tsarewa. ‘Yan sanda sun bayyana cewa ana ci gaba da bincike kan lamarin tare da tura shari’ar zuwa sashen binciken kisan kai na Iyaganku.
