Saƙon Kirsimeti: Gwamnatin Tarayya ta rage farashin sufuri a hanyoyi 144 – Tinubu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce Gwamnatin Tarayya ta samar da tallafi ga harkar sufuri a yunƙurita na rage raɗaɗin talauci a lokacin bukukuwan ƙarshen shekara.

A yayin saƙonsa na Kirsimeti, Tinubu ya ce gwamnati ta samar da sufurin jiragen ƙasa kyauta da kuma ragi ga sufurin motoci a yayin tafiye-tafiye ga ƴan Nijeriya a lokacin bukukuwan.

Tinubu ya kuma tabbatar wa al’umma cewa hanyoyi za su kasance cikin tsaro, ya na mai cewa sun samar da sauƙin tsadar ababen hawa a titina 144 a sassa daban-daban na faɗin Nijeriya.

Ya yi kira ga kiristoci da su yi wa shugabannin da ma ƙasa baki ɗaya addu’a a yayin bukukuwan nasu.

Kazalika, ya yi kira a gare su da su yaɗa soyayya haɗin-kai da zaman lafiya a tsakaninsu domin kai Nijeriya ga nasarorin da take fatan cimma yayin da su ke cigaba da ƙoƙarin farfaɗo da tattalin arziƙi.

By Babaji