Mahaifiyar gwamnan Jigawa ta rasu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A safiyar ranar Laraba ne Mahaifiyar Gwamnan Jihar Jigawa (Umar Namadi), Hajiya Maryam Namadi ta rasu.

Sakataren Labaran gwamnan, Hamisu Mohammed Gumel ya faɗi hakan a wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce za a gudanar jana’izarta ne a yammacin ranar kamar yadda addinin musulunci ya tanadar a garin Kafin Hausa.

Gwamnan da iyalansa sun buƙaci al’umma da su sanya ta a cikin addu’o’insu don samun rahamar Allah SWT.

By Babaji