Rundunar Sojin Ruwan Nijeriya ta gina asibitin zamani kyauta a Zariya

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar Sojin Ruwa ta Nijeriya ta gina asibitin neman lafiya a matakin farko ga al’ummar Samaru da ke Zariya a wani ɓangare na ayyukan tallafin gaggawa na ofishin rundunar sojin ruwa ta Nijeriya.

A cewar mataimakin CNS, ɓice Adm. Emmanuel Ogalla, a yayin ƙaddamar da aikin a ranar Juma’a, ya ce, an gudanar da aikin ne domin tunawa da Rear Adm. Ibrahim Dewu.

A yayin taron ya samu wakilcin muƙaddashin shugaban sashen Kawo cigaba Rear Adm. Julius Nwagu.

A cewarsa, samar da cibiyar lafiya abu ne muhimmi da zai inganta rayuwar al’ummar Samaru.

Ogalla ya ce wannan aiki ya nuna yadda rundunar sojin ruwa ke ƙoƙarin tallafa wa harkar lafiya da samar da ingantaccen kiwon lafiya.

Daga nan ya taya Dewu murna saboda gina cibiyar lafiya inda ya ce, “gina wannan cibiyar lafiyar wata hanya ce ta inganta alaƙa tsakanin sojoji da al’ummar gari da suka ci moriyar waɗannan ayyuka.

“Ya ce wannan na daga cikin manufa ta samun goyon bayan al’ummar yankin a dukkan wajen tabbatuwar nasarar rundunar na ƙoƙarinta na samar da zaman lafiya a ƙasa bakiɗaya.”

“A kan haka ne rundunar ta amince da wannan aiki da faɗaɗa cibiyar lafiyar” ya faɗa.

A nasa ɓangaren gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, wanda babban sakataren kiwon kula lafiya a matakin farko, Farfesa Bello Jamo, ya gode wa rundunar sojin ruwa ta Nijeriya kan wannan aiki.

Sani ya ce wannan aiki ne mai muhimmancin gaske wajen inganta harkar lafiya a jihar da ma ƙasa bakiɗaya.

Ya ce inganta cibiyar lafiya ta Samaru alama ce ta haɗin guiwa da ke tsakanin jihar Kaduna da rundunar sojin ruwan da ma sauran masu ruwa da tsaki da ke ƙoƙarin ganin an inganta harkar lafiya.

A cewarsa, samun damar ingantaccen lafiya abu ne mai muhimmanci ga gwamnatin jihar Kaduna musamman ta fuskar lafiyar mata masu juna biyu da kiwon lafiyar ƙananan yara da cututtuka da inganta lafiya a matakin farko.

“A yau wannan aiki na nuna cewa an samu cikgana da zai ba wa al’ummar Samaru damar samun ingantacciyar lafiya.”

“Muna matuƙar godiya ga rundunar sojin ruwa ta Najeriya saboda faɗaɗa wannan asibiti a zahiri.”

“Wannan shiri na ba da tallafi ga al’umma ‘yar manuniya ce game da irin jagorancin rundunar wajen inganta alaƙarta da al’umma ta hanayar samar musu da ayyukan cigaba,” inji gwamnan.

By ukarofi