
Daga BELLO A. BABAJI
Kamfanin tace dangogin mai na Warri (WRPC) dake Jihar Delta ya fara aiki.
Shugaban Kamfanin Man fetur na Ƙasa (NNPCL), Mele Kyari ya bayyana hakan a yau Litinin, a lokacin da ya kai ziyarar gani da ido a matatar.
Ya ce duk da cewa ba a kai ga kammala aikin 100 bisa 100 ba, amma an fara ayyukan tace mai.
Ya kuma tabbatar wa masu kokwanto game da aikin matatar kan cewa tabbasa abu ne mai yiwuwa ba kamar yadda su ke ɗauka ba na rashin yiwuwar sa.
Hakan na zuwa ne makonni kaɗan bayan matatar Fatakwal mai fitar da ganga 60,000 a kowacce rana ta dawo aiki.
